Saduwar Aure: Muhimmanci, Fa’ida da Tasirinta ga Zaman Aure Mai Dadi
Saduwar aure wata babbar ibada ce kuma ginshiki mai ƙarfi a cikin rayuwar aure. Ita ce hanyar da Allah Ya halatta wa ma’aurata su kusanci juna cikin soyayya, natsuwa da jin daɗi. Idan saduwar aure ta samu matsala, to babu shakka hakan na iya haifar da tangarda mai tsanani a zaman aure, wadda ka iya janyo rashin fahimta, nesa tsakanin ma’aurata, ko ma rugujewar aure gaba ɗaya.
Abin lura shi ne, sau da dama idan ana magana kan matsalar saduwar aure, ana ɗora laifin ne a kan mata kawai. Wasu suna cewa mace ba ta da sha’awa, wasu kuma na ganin mace ba ta iya biyan bukatar mijinta. Amma gaskiyar magana ita ce, saduwar aure al’amari ne na ma’aurata biyu, ba na mace ko namiji shi kaɗai ba.
Me ake nufi da Saduwar Aure?
Saduwar aure na nufin kusantar jiki da zuciya tsakanin miji da mata bisa k...
