Kalolin Kwanciyar Aure: Nau’o’in Zaman Lafiya Tsakanin Ma’aurata
Aure wata hanya ce da Allah Ya tanadar domin maza da mata su rayu tare cikin soyayya, tausayi da fahimtar juna. Amma babban buri a cikin aure shi ne kwanciyar aure, wato rayuwa cikin zaman lafiya da natsuwa tsakanin ma’aurata. Duk da cewa mutane da yawa suna shiga aure da wannan fata, ba kowa ne yake samun kwanciyar aure ba.
Dalilin hakan shi ne wasu ma’aurata ba su san yadda za su kula da dangantakarsu ba. Wasu kuma suna manta da abubuwan da suka gina soyayya tun kafin aure, kamar kulawa, magana mai dadi da girmama juna. Da zarar an yi aure sai wasu su sauya hali, wanda hakan kan haifar da sabani ko rashin jituwa.
A gaskiya, kwanciyar aure tana da kaloli ko nau’o’i da dama, kuma duk wani gida mai zaman lafiya yana ginuwa ne a kan waɗannan ginshiƙai. Idan ma’aurata suka fahimci wadan...
